Sabon shugaban kasar Gambia ya nada wata mata Mataimakiya
– Sabon shugaban kasar Gambia ya nada mace a matsayin mataimakiyar sa
– Adama Barrow ya zabi Fatoumata Tambajang a matsayin ta biyu
– Kwanan nan Barrow ya hau mulki bayan Jammeh ya sauka da karfi da jiya
Sabon Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow ya nada Fatoumata Tambajang a matsayin Mataimakiyar sa. Halifa Sallah, mai magana da bakin Barrow ya bayyana haka a wani taro da aka yi jiya da manema labarai a Garin Banjul.
Fatoumata tayi kokari wajen sasanta abokan gaban siyasa a zaben bara. Fatoumata tayi aiki a matsayin mai bada shawara a kan harkokin mata da yara lokacin Shugaba Dawda Jawara. Ta kuma rike Shugaban Majalisar matan Kasar. Fatoumata dai tana da kyautar lambar girma bayan hidimar da tayi wa Kasar.
KU KARANTA: Tarihin Sarakuna mata da aka yi a baya
Kwanan nan Yahaya Jammeh ya sauka da karfi da yaji bayan dakarun ECOWAS sun dura cikin Kasar. Ko shi dai Mataimakiyar sa a lokacin mace ce, wanda tayi murabus daga kujerar da rikicin siyasar nan ta taso.
A Najeriya kuma a watan Maris mai zuwa ne Minista Amina J. Mohammed za ta tattara ina ta-ina ta ta bar Najeriya ta koma Majalisar Dinkin Duniya watau UN. An nada Amina Mohammed da wasu matan biyu babban mukami a Majalisar kwanaki.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook
https://www.facebook.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng