Kulop din Barcelona ta yi hasarar Busquets saboda rauni
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta yi babban hasarar dan wasanta Sergio Busquets bayan da ya ji rauni a dunduniyarsa a karawarsu da kulob Eibar a ranar Lahadi a bayan sun ci 4 - 0
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ga samu, ta kuma ga rashi bayan da ta lallasa Eibar ta ci 4 da nema, a karawarsu na ranar Lahadi, amma kuma ta yi hasarar Sergio Busquets wanda zai dade bai buga kwallo ba bayan raunin da ya ji a yayin karawar.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta yi babban hasarar dan wasanta Sergio Busquets bayan da ya ji rauni a dunduniyarsa a karawarsu da kulob Eibar a ranar Lahadi a bayan sun ci 4 - 0
Dan wasa Sergio mai shekara 28 da haihuwa, wanda kuma tauraruwarsa ke haske a Barcelona, an fita da shi ranga-ranga daga fili a gadon daukar maras lafiya na tafi-da-gidanka, bayan kimanin mintuna 8 da soma wasa, bayan sun yi taho mu gama da Gonzalo Escalente.
Sakamakon gwaje-gwajen likita ya nuna cewa, Sergio dan wasan mai buga tsakiya, ya gurde kafarsa ne a inda dunduniyarsa ta tabu, kuma da alamu zai dade yana jinya kafin ya koma buga kwallo.
Wasu rahotanni daga Spain na cewa, dole ce za ta sa a jingine dan wasan na tsawon akalla makonni biyu, wanda hakan zai sa ba za a buga wasan kusa-da-na-kusa da na karshe ba watau kwata final, na gasar Copa del Rey da shi ba, a inda kulop dinsa zai kara da Real Sociedad a ranar Alhamis.
Raunin kuma ya haddasa masa rashin samun dama taka leda a karawar da kulop din sa zai yi a gasar La Liga, a in da za su kara da Real Betis, da Athletic Bilbao, sai dai mai horas da ‘yan wasan Barcelonan Luis Enrique na fatan Sergio zai murmure kafin karawarsu da kulop din PSG a gasar cin kofin zakarun turai wanda za a buga 14 ga watan Fabarairu.
Asali: Legit.ng