Farashin man diesel na kara hauhawa

Farashin man diesel na kara hauhawa

A Najeriya tsadar man diesel ko kuma man gas na cikin abubuwan da ke addabar masu sufuri musamman na manyan motoci da masu kanana da matsakaitan masana'antu har ma da wasu kamfanoni da ke sarrafa kayayyaki.

Farashin man diesel na kara hauhawa
Farashin man diesel na kara hauhawa

A yanzu haka dai man na diesel ya fi kowanne daga cikin nau'ukkan albarkatun mai tsada a kasar inda farashin sa ya kama daga Naira 180 zuwa 270 a kan kowacce Lita a gidajen mai.

Wani mamba a kungiyar dillalan mai masu zaman kansu a Najeriya IPMAN, Alh.Abubakar Abdullahi Zangon-daura ya shaidawa majiyar mu cewa abin da ke haifar da tsadar man na diesel shi ne saboda rashin wadatarsa, domin idan da har ya wadata ba zai yi tsada ba.

Baya ga farashin man diesel da ya yi tsada a Najeriyar, al'ummar kasar ma na kukan tashin goron zabi da farashin man kananzir ma ya yi.

A wasu lokutan dai idan aka samu tsadar kowanne nau'in mai a kasar, a kan dora laifin a kan dillalan man inda ake zarginsu da boyewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: