Dalilin da ya sa ba zamu saki Zakzaky ba - Buhari

Dalilin da ya sa ba zamu saki Zakzaky ba - Buhari

- Fadar Shugaban kasa ta jaddada cewa ba za a saki Shugaban Kungiyar Shi'a ta kasa, Malam Ibrahim El Zakzaky ba saboda batun sakinsa ya jibinci sha'anin tsaron kasa da kuma ra'ayoyin jama'ar kasa.

- Fadar Shugaban kasa ta yi nuni da cewa sha'anin El Zakzaky ya wuce batun kotu kuma dokar kasa ta fifita tsaro da kuma ra'ayin jama'ar kasa a kan bukatar wani mutum guda.

Dalilin da ya sa ba zamu saki Zakzaky ba -Buhari
Dalilin da ya sa ba zamu saki Zakzaky ba -Buhari

A cewar Fadar Shugaban kasa, Uwargidan El Zakzaky wadda ke tare da shi a inda ake tsare da shi, za ta iya yin tafiyarta saboda jami'an tsaro sun tsare ta ne saboda duba lafiyarta don ta samu rauni a lokacin da aka kai samame gidan mijin nata.

A kwanan baya dai Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya ta bi umurnin kotu ta saki jagoran Shi’a Ibrahim Zakzaky da daruruwan mabiyan shi da ake tsare da su.

KU KARANTA KUMA: Likitoci za su sa kafar wando daya da yan sanda a Zamfara (DALILI)

A yau ne wa’adin kwanaki 45 da kotun Abuja ta ba gwamnati zai kawo karshe.

Daraktan Amnesty a Najeriya Makmid Kamara ya ce hakan zai tabbatar da gwamnati ta raina doka idan har ta yi watsi da bin umurnin kotu.

Zakzaky ya shafe tsawon shekara guda a tsare tun lokacin rikici tsakanin mabiyan shi da Sojojin Najeriya a Zaria.

‘Yan Shi’a sun ce an kashe ma su mambobi akalla 350, alkalumman da sojojin Najeriya suka musanta.

A jiya Litinin ne dai wa’adin kwana 45 da babbar kotun taraiyar Nijeriya ta yanke a saki jagoran ‘yan Shi’a Ibrahim Elzakzaky ke cika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng