Manchester United ta fi kowa kudi a Duniya

Manchester United ta fi kowa kudi a Duniya

– Yanzu Kungiyar Manchester United ta fi kowa kudi a Duniya

– Man Utd ta buge Kungiyar Real Madrid da Barcelona

– Leicester City sun samu shiga sahun kungiyiyi masu kudi

Manchester United ta fi kowa kudi a Duniya
Manchester United ta fi kowa kudi a Duniya

Kungiyar kwallon kafan Man Utd ta Ingila ta kerewa kowace Kungiya kudi yanzu haka a Duniya. Man Utd ta doke Real Madrid wanda ke kan gaba a da shekara da shekaru. Real Madrid dai ta dawo na uku a jerin masu kudin Duniya.

Kungiyar Man Utd na da kudi har Dalar Euro Miliyan €689, sai kuma Kungiyar Barcelona ke biya da Miliyan €620.2 yayin da Real Madrid ke da Miliyan €620.1 a yanzu. Kungiyar nan ta Bayern Munich da ke Jamus ce ta hudu, sannan kuma Man City tana ta biyar.

KU KARANTA: Shugaban Kasa ya tafi hutu

Duk Duniya dai yanzu babu Kungiyar da ke jawo kudi irin Manchester United. Kungiyar Madrid dai ta fi shekara goma tana zuwa ta daya, sai dai bara Man Utd ta buge ta. Sauran Kulobs da suke cikin jerin sun hada da: Leicester, Inter Milan, West Ham, Schalke, AS Roma, Tottenham, Dortmund, At. Madrid, Arsenal, Liverpool, Juventus, dsr.

Kungiyyoin kwallon kafa na Ingila dai sun taka rawar gani bana. Wannan ne dai karo na farko da Man Utd ta zo ta daya tun shekarar 2003.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng