Tarihin mai gadin da ya zama shugaban kasar Gambia
Sabon shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, fitaccen mai saye da sayar da gidaje ne, wanda bai taba rike wani mukami na siyasa ba kafin kayen da ya yi wa Shugaba Yahya Jammeh a zaben watan Disamba.
An haife shi ne a shekarar 1965 a wani kauye da ke kusa da garin kasuwancin nan na Basse a gabashin kasar.
Kafin a tsayar da Mr Barrow, mai shekara 51, a matsayin dan takarar shugaban kasar, ya kwashe sama da shekara goma yana hada-hadar gidaje.
Ya zauna a birnin Landan a shekarun 2000, lokacin da yake karatu kan harkokin gidaje, kuma a lokacin ne ya yi aiki a matsayin mai gadin babban kantin nan na sayar da kaya, Argos a arewacin Landan.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya sa yan Najeriya sun shiga kangin bauta – Kungiyar matasan Arewa
Ya koma kasar Gambia a shekarar 2006 inda ya soma kasuwanci a fanni gine-ginen gidaje.
A lokacin da yake yakin neman zabe, Mr Barrow ya sha sukar Shugaba Jammeh kan rashin sanya wa'adi biyu kawai ga duk wanda zai shugabanci kasar sannan ya soki daurin da aka yi wa 'yan jam'iyyun hamayya.
Mista Barrow yana fafutikar ganin bangaren shari'a ya samu 'yanci sannan 'yan jarida da kuma kungiyoyin farar-hula sun samu damar fadin albarkacin bakinsu ba tare da wata shakka ba.
Ya ce zai kafa gwamnatin hadaka ta shekara uku wacce za ta kunshi jam'iyyun hamayya idan ya ci zaben.
Jammeh ba shi da imani, sannan ya sha alwashin soke dukkan shirye-shiryen da yake aiwatarwa.
KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya na danasanin zaban Buhari – Makarfi
Ya kara da cewa kasar za ta koma cikin kungiyar Commonwealth da kuma kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya, ICC.
Mista Barrow dai mutum ne da sai ya tauna magana kafin ya yi ta, kuma ba shi da irin zaƙin maganar nan da ke jan hankalin masu saurarensa.
Sabon shugaban na Gambia Musulmi ne wanda ke da mata biyu da 'ya'ya biyar.
Asali: Legit.ng