Dalibin jami’ar Maiduguri ya ƙera ƙaramar mota mai aiki da ƙwaƙwalwa
Wani dalibin a tsangayar koyar da kimiyya da fasahar kerekere na jami’ar Maiduguri mai suna Haruna Abubakar ya kera wani na’aurar mai aiki da kwakwalwa tare da wani na’urar daka iya gano sinadarin giya, wanda za’a iya sanya shi a motoci.
Haruna ya bayyana wadannan kayan kerekeren nasa ne a yayin zaman kungiyar su na daliban jihar Borno masu sha’awar kimiyya da fasaha mai suna ‘Borno Tech Forum’ inda suke ganawa duk bayan wata guda don kara ma juna sani.
KU KARANTA:Sakonni 5 da Shekau ya aika ma shugaba Buhari
Matasan sun kirkiri kungiyar ne don samar da wata kafa ko dandali inda matasan jihar Borno masu sha’awar kerekere zasu dinga haduwa da takwarorinsu don kara ma juna sani tare da tattauna batutuwan da zasu samar da cigaba a jihar tasu, musamman ta fannin kimiyya da fasaha.
Zuwa yanzu dai Abubakar yace sun gudanar da zaman tattaunawa sau 2, a yayin taron nasu wani dan kungiyar Abubakar Dala ya nuna musu na’urar nika tumatir da aka fi sani da suna ‘Blender’, sa’annan ya nuna ma abokansa wata tsarin kirga gidaje da filaye da ya hada akan na’aura mai kwakwalwa wato komfuta.
A gaskiya a kulli yaumin ana samun hazikan matasa yan Najeriya dake baiwa duniya mamaki sakamakon fikira da bsirar su. kimanin watannin biyu da suka gabata ma an samu wani yaro dan jihar Ebonyi Ihere-serg Mascot daya kera mota mai amfani da hasken rana.
Ga bidiyon abubukar:
Asali: Legit.ng