Abubuwa 10 masu zafi da Shugaban Boko Haram Shekau ya fada a sabon faifai kan harin da suka kai masallacin jami’ar Maiduguri
A yammacin ranar Litinin, 16 ga watan Janairu, wani faifai ya billo dauke da sautin shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, inda ya bayar da sanarwan cewa suke da alhakin kai harin bam din da ya tashi a masallacin jami’ar Maiduguri (UNIMAID).
Shugaban na kungiyar yan ta’addan Boko Haram din, ya bayyana cewa sun kai harin bam din ne saboda wasu abubuwa da ake aikatawa a masallacin wanda yayi karo da koyarwan addinin musulinci.
KU KARANTA KUMA: Kwanakinka sun kusa karewa, yan Najeriya sun maida martani yayinda Shekau ya bayyana dalilin da yasa aka kai hari UNIMAID
Ga wasu daga cikin abubuwan da ya fada:
1. Karda ma ku yaudari mutane kuce masallaci ne, ina masallacin da ake kafirci a ciki, annabi ya taba yin wani abu mai kama da ‘democracy’ ne a cikin masallacin sa?
2. Kuna cin amanar annabi Muhammadu ku gina masallaci kuna aikin yahudawa a ciki, idan aka ce maku ba kyau sai ku dunga cewa kuna son annabi.
3. Zamu kara yi bazamu tsaya ba, bazamu iya kallon wanda ke chakuda musulunci da kafirci ba, Karya ne ba musulmi bane.
4. Buhari ba haushin ka muke ji ba, Kukasheka Allah ya sheke ka, ba haushinka muke jiba. Yan Najeriya ba haushinku muke ji ba, abunda kukeyi da sunan ibada ne yasa muke jin haushin ku
5. Ku yan adawarmu ne a yanzu, duk wanda ke kafirci Allah yace inyi adawa dashi. Mune muka tayar da bam din kuma karyanku, kun kwashi kashinku a cikin satin da muke ciki.
6. Bamu ma fara addinin Allah ba, mu fata ma mukeyi Allah ya karba, a tunaninku sai kun kashe mu ne zaku ci nasara, karya kuke yi.
7. Muna fatan Allah karda yasa mu chanja, Allah ya kashe irin wadannan munafukai masu cin amana a cikin masallaci
8. Ku ba malamanmu bane , Qur’ani ne malaminmu, aikinku yafi luwadi, banza masu hukunta hukuncin luwadi.
9. Mun tada bam saboda Buhari yace zamu sa kafar wando daya dashi, kai (Buhari) baka kai fada bama domin ni (Shekau) da karfin Allah nake fada. Ina kai ina karfin Allah Buhari, Ina kai ina karfin Allah Obama sannan ina kai ina karfin Allah Donald Trump?
10. Idan kun isa kuna son ku hallakar damu kuce abunda mukeyi baya cikin littafi idan ba haka ba kun shiga uku, wallahi sai kun mutu da bakin ciki.
Saurari cikakken sautin:
Asali: Legit.ng