Mustapha Indimi yayi wa matarsa Fatima Sheriff wankan naira dubu-dubu a gurin bikinsu
1 - tsawon mintuna
Mustapha Indimi, dan biloniya, Mohammed Indimi yayi aure a ranar Asabar, 14 ga watan Janairu da masoyiyarsa Fatima Sheriff, yarinyar dan majalisar wakilai, Mamman Nur Sheriff, a masallacin Indimi, Maiduguri.
KU KARANTA KUMA: Kifi mai dauke da rubutun larabci (hotuna)
Bidiyon sama na nuna lokacin da Mustapha yayi Amaryarsa wankan naira dubu-dubu (N1000) a gurin aurensu.
KU KARANTA KUMA: Abu mai taba zuciya: Kalli kyakyawan jaririn da aka yasar a makabarta
Manyan mutanen da suka halarci bikin sun hada da Gwaman jihar Borno. Kashim Shettima, mataimakinsa, Hon Usman Durkwa, Sanata Ali Ndume, tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Sani Yerima.
Asali: Legit.ng