An nada sabon Shugaban Jami’ar Kaduna
– Jami’ar KASU ta Kaduna ta nada sabon Shugaba
– Farfesa Mohammed Tanko ne sabon Shugaban Jami’ar
– Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da nadin
A jiya ne gwamnan jihar Kaduna, mai girma Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya tabbatar da nadin Farfesa Mohammed Tanko a matsayin Shugaban Jami’ar ta Jihar Kaduna watau KASU. Wannan ya biyo bayan mataki da Hukumar kula da Jami’ar ta dauka
Farfesa Tanko dai Malamin Jami’ar ne tun asalin sa, ya rike Shugaban sashe da Tsangayan Tattali na Makarantar da kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar a baya. Kai bari ma dai ya taba rike Mukaddashn Shugaban Jami’ar a wani karo, don haka ya san harkar Jami’ar ciki-da-bai.
KU KARANTA: Mai Digiri ya zama Mai shayi
An haifi Mohammed Tanko ne a Kawo, Farfesa ne a bangaren akawu. Tanko yayi Digirin san a farko a Jami’ar Bayero ta Kano a fannin Ilmin akawu, daga nan yayi digirgir da kuma MBA a shekarar 2000. A shekarar 2005 Tanko ya kammala karatun Digiri na uku a Jami’ar ABU Zaria.
Farfesa Tanko kwararren Akawu ne, ya kuma rike matsayi da dama har a Gwamnatin Jihar Kaduna, ya kuma yaye dalibai masu karatun Digiri da dama. Yana da rubuce-rubuce masu yawan gaske.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook
Asali: Legit.ng