Magidanci ya zargi matarsa da maita, yace zata kashe shi

Magidanci ya zargi matarsa da maita, yace zata kashe shi

Wani dan jarida a kasar Malawi mai suna Collins Mtika ya daura hoton matarsa a kafar sadarwar zamani ta Facebook inda yayi ikirarin cewar mayyace.

Magidanci ya zargi matarsa da maita, yace zata kashe shi
Collins Mtika

Jaridar Malawinewsnow ta ruwaito cewar ba wannan bane karo na farko da dan jarida Collins Mtika ke tozarta matarsa a kafar sadarwa ta Facebook ba.

KU KARANTA:Faston daya damfari mabiyansa kudi ya shiga komar yansanda

Sai dai a wannan karon, dangin matar sunce ta ji ciwon kalaman da mijin nata ya furta akanta, inda a yanzu haka tana cikin wani mawuyacin hali, duk da haka, majiyar mu ta shaida mana matar bata da niyyar daukan wani mataki akan Collins, domin tace yana da ciwon tabin hankali.

Magidanci ya zargi matarsa da maita, yace zata kashe shi
Matar Collins

Shi dai Collins Mtika ya daura hoton matarsa ne a Facebook inda yayi ma hoton taken “wannan itace mayyar dana auro, wata rana sai ta kashe ni.”

KU KARANTA:Barayin bunsuru sun sha horo mai tsanani

Hoton Facebook din ya watsu sosai, inda wasu ma har daukan sa suke yi hoto don kara watsawa, amma dai daga bisani Mtika ya sauke hoton daga kafar ta sadarwa.

Ku cigaba da bibiyan labaran mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel