Arsenal ta sayi dan wasa na farko a sabuwar shekarar 2017
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake Ingila ta kammala cinikin wani sabon dan wasa Cohen Bramall daga kungiyar Hednesford Town dake rukunin na biyu a gasar cin kofin Firimiya na arewacin kasar Ingila.
KU KARANTA:Olivier Giroud ya ci ma Arsenal wata mahaukaciyar kwallo da bayan kafa (bidiyo)
Arsenal ta sanar da siyan dan wasan ne mai shekaru 20 bayan ya nuna bajinta a jarabawar da yazo yayi a kungiyar. Ana sa ran Bramall zai fara wasa a rukunin yan kasa da 23 na kungiyar ta Arsenal.
Sai dai Cohen Bramall zai yi wasa a karkashin mai horarwa Steve Gatting, a baya ma ya buga wasa tare da shahararren dan wasa Market Drayton a kakar wasa data gabata.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng