An kama mahaukaci yana kokarin sace yara biyu a Delta (hotuna)
1 - tsawon mintuna
An kama wani mutumi dake karyan hauka a hanyar Utagbaunor/umukwata, karamar hukumar Ukwani dake jihar Delta.
A cewar wani mai amfani da shafin Facebook Ossai Ovie Success, an kama shi ne a lokacin da yake yunkurin satan yara biyu. Ance wanda ake zargin yama kusan kashe daya daga cikin yaran, kafin a kawo agaji.
KU KARANTA KUMA: Akwai jita-jita cewa Rahama Sadau zata dawo Kannywood
“Yan sanda sun kama me karyan haukan. Godiya ga DPO na Obiaruku kan kawo dokin gaggawa. An kai yaron da aka kai ma hari asibiti.”
Asali: Legit.ng