Likitocin Asibitin Aminu Kano sun dawo aiki
– Likitoci sun janye yajin-aikin da suka shiga a Asibitin koyarwa na Aminu Kano
– A da Malaman Asibitin sun tafi yaji da din-din-din
– Likitoci za su koma aiki gadan-gadan yau
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Malaman Asibitin Malaman Aminu Kano watau AKTH sun janye yajin-aikin da suka shiga kwanaki. A baya dai Ma’aikatan Asibitin na Malam Aminu Kano sun shiga wani yaji na sai Inna-ta-gani.
Shugaban Kungiyar Malaman Asibitin, Kwamared Abulrahman Aminu ya bayyanawa majiyar mu cewa za su dawo aiki a yau watau ranar Talata. Aminu yace hakan ya biyo bayan wata tattaunawa da suka yi da Ma’aikatar lafiya da kuma Hukumar Asibitin na koyar da Dalibai na Malam Aminu Kano.
KU KARANTA: Bam ya tashi a Maiduguri; an hallaka
Likitocin dai sun tsaida yajin aikin ne na mako biyu, sai dai idan har makonnin suka cika ba tare da an yi wani abu a kai ba, za su koma wani yajin kuma na din-din-din. Ma’aikatan dai sun tafi yajin aikin ne a Ranar Asabar. Wani daga cikin marasa lafiya yake cewa an sallame su daga Asibitin a wancan lokaci.
Haka dai kwanaki Likitocin Asibitin koyan-aiki na Jami’ar Ahmadu Bello suka yajin-aiki na din-din-din. Kungiyar Likitocin Asibitin da ke Shika, a Jihar Kaduna sun shiga yajin aikin ne bayan an gaza biya masu bukatun su.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook
Asali: Legit.ng