INNALILAHI WAINAILAIHI RAJIHUN: Tsoho gwamna jihar Niger ya rigamu gidan gaskiya
Tsohon gwamnan jihar Niger injiniya Abdulkadir Kure ya rasu a wata asibiti a kasar Jamus.
Allah ya wa tsoho gwamnan jihar Niger injiniya Abdulkadir Kure rasuwa a wata asibiti a kasar Jamus.
An samu wannan sanarwa ne daga iyalan shi marigayin tsohon gwamnan a cewan su Allah ya masa cikawa ne a wata babban asibiti ta kasar Jamus.
Wata rohoto daga jaridan Nation na cewa an kai wannan tsohon gwamna kasan waje a mako da ya gabata sanadiyan wata rashin lafiya.
Marigayin ya yi wa’adin gwamnati jihar Niger zo biyu daga shekara 1999 har zuwa 2007.
Gwamnan na 12 a jerin tsofofin gwamnonin jihar Niger, kuma yana na 3 a cikin tsofofin zababbu gwamnonin farar hula bayan mai martaba sarki Awwal Ibrahim daga shekara 1979 – 1983 da dokta Musa Inuwa daga shekara 1992 – 1993.
A cikin furucin kwamishinan bayanai, al'adu da yawon shakatawa, Jonathan Vatsa, a garin Minna babban birnin jihar Niger a daren ranar lahadi, a watan Janairu 6, 2017. Gwamnatin jihar ta sanad da ranaku uku na zaman makoki.
A cewar kwamishinan, gwamnan jihar Niger Abubakar Bello ya ba maikatan jihar Niger hutu a ranar jana’izan tsohon gwamnan saboda jama’a su samu hallarta bikin jana’izan.
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa da http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng