Wanene sabon shugaban kasar Ghana

Wanene sabon shugaban kasar Ghana

– An rantsar da Nana Akufo-Addo a matsayin sabon shugaban kasar Ghana

– Nana ya doke John Mahama daga kujerar sa

– Shin wanene ma Nana Akufo-Addo?

Wanene sabon shugaban kasar Ghana
Wanene sabon shugaban kasar Ghana

A Jiya 7 ga wannan watan ne aka rantsar da Nana Akufo-Addo a matsayin sabon shugaban Kasar Ghana. Nana Akufo-Addo ya doke shugaban kasa John Dramani Mahama daga kan kujerar sa a zaben da aka gudanar a watan Disamban bara.

Shin wai wanene sabon shugaban kasar ta Ghana? Wanda ya shigo da wayar salula cikin Ghana?

An dai haifi Nana a tsakiyar Accra, shekaru 72 da suka wuce. Mahaifin sa Edward Akufo-Addo yana cikin Alkalan farko na Kasar ya kuma rike shugabancin Kasar daga shekarar 1969 zuwa 1972. Nana dai yayi karatu a Gida da kuma Kasar Ingila.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ba zai samu nasara ba

A shekarar 1975 ya shiga Kotu bayan ya karanci Ilmin tattali da kuma shari’a a Ingila. Yayi aiki a wurare da dama har da Amurka. Akwai ma dai lokacin da ya rike Ministan shari’a na Kasar Ghana. Addo dai tun yana shekara 30 a Duniya yake siyasa.

Nana Addo dai ya dade yana neman takarar shugabancin Kasar tun a shekarar 1998. Sai dai wannan karo ya samu.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel