Bacin rai guda 6 na wadanda suka kammala karatun Digiri a Najeriya

Bacin rai guda 6 na wadanda suka kammala karatun Digiri a Najeriya

Idan kana jin rayuwar ka tana cikin kunci, ya kamata ka karanta abin da wani dalibi da ya kammala jami'a a Najeriya ya rubuta. Za ka san me ake nufi da rayuwa ba aikin yi bayan kammala jami'a.

Bacin Rai Guda 6 na wadanda suka kammala karatun Digiri a Najeriya
Bacin Rai Guda 6 na wadanda suka kammala karatun Digiri a Najeriya

Idan ka samu damar yin hira da yaran da suke karatu a jami'a, saka ji yadda suke da buruka. Sun tsara duk abinda suke fatan zama a rayuwar su bayan kammala karatu. Amma abin da suke cin karo dashi bayan kammala Karatu yakan dimanta su.

Ga wasu daga cikin matsalolin da daliban ke cin karo da su:

1- Gano cewa shaidar kammala digiri ba komai ba ce face wata takarda gama-gari: Daya daga cikin matsalolin da dalibai ke cin karo da su shi ne, gano cewar takardar shaidar digiri da su ka yi ta wahala a kanta dare da rana ba komai bace face gama-garin takarda.

2- Bayan shafe tsawon lokaci na neman aiki: ba tare da an samu ba, jin kan cewa na kammala jami'a zai kama gabansa. Wannan fafutukar ta neman aiki ba tare da samu ba za ta sa ya fara rasa duk wani fata. Damuwar su na karuwa sanda suka ga suna ayyuka iri daya da wadanda basu kama kafar su a ilimi ba.

Kar ka damu da yawa idan ka tsinci kanka a irin wannan hali. Yi kokari ka koyi wani abu da zai sa rayuwar ka ta zama mai ma'ana cikin al’umma.

2- Rashin aiki na sa mutum ya ji rayuwar sa bata da wani muhimmanci: Duk yanda ka ke ji da kai a matsayin mai digiri idan baka da aiki sai ka rasa kimarka. Idan baka samun wani cigaba a gurin aikin ka, rayuwa cikin al-umar ka ma sai tayi maka wuya. Halartar shagulgula sai yayi maka wahala idan mafi yawan su ma'aikata ne.

Mara sa aiki bayan kammala jami'a su zakai ta gani wuraren bauta suna ta addu'ar samun aiki. Su ake fara zargi lokacin da aka rasa wani abu a gidajen makwabta.

Masu bada rance basa san basu bashi dan kuwa ba'a san sanda zasu iya biya ba idanma zasu iya biya din.

Bayan wadannan matsaloli na samun aikin yi, samun masoyiya shima wata babbar kajaga ce. Iyaye basa bada "yar su ga wanda bai da aikin yi.

3- Zabar abin da mutum ke san karata ba shi da wata ma'ana: Za ka sha mamakin yadda a karshe aikin ka zai bambanta da abin da ka karanta. Wannan kuwa yana da alaka ne da yadda dalibai ke shan wuya wajen neman aiki wanda a karshe yake jawo su rungumi duk abida yazo musu. Ga wadanda ke da sha'awar san wani darasi, rashin samu aiki na jawo rasa sha'awar wannan darasi.

Haka zalika, kammala karatu da wata shaidar takarda mai daraja kaza bai lallai yayi wani amfani ba tunda dai su kamfanoni na da nasu tasre-tsaren daukar aiki. Za'a iya daukar mai shaidar takarda ta uku a bar mai ta biyu koma mai ta daya.

4- Fadawa tarkon "yan damfara: Zaman gida babu aikin yi yana da ciwo. Sau da yawa wannan yakan jawo dalibi ya fada tarkon "yan danfara sakamakon idon sa da ya rufe wajen neman aiki. Wasu daliban na iya tsintar kansu a matsayin wadanda ake garkuwa dasu ta yanda za'a bukaci biyan kudin fansa kafin sako su.

5- Tsammanin da ake maka na taimakawa:

Da zarar ka kammala jami'a, dan taimakon da kake samu daga gida zai tsaya or ya ragu. "Yan uwa zasu fara tunanin taimakon ka duk da baka da aiki. Zasu dinga ganin cewa, yanzu kai ya kamata ka taimaka kamar yanda suka taimaka maka dan ganin kayi karatu. Gazawa wajen sauke nauyin ka zai sa suji ka basu kunya.

Wannan zai zama kari ne akan matsalolin da kake fuskanta daga wajen abokai da za suyi ta bijiro maka da bukatu.

Idan wannan ta faru dalibi zai ji kamar ana zolayarsa yayin da "yan uwa suma na da nasu ra'ayin.

6- Rasa matsayin ka:

Babu wata ma'ana cikin kafafar nuna cewa kai ka yi digiri idan ba ka samu aiki ba. Rasa aiki nasa dalibi zubar da duk wata takamar kasancewa mai ilimi sannan ya mai da shi zuwa matakin mai gantali akan titi. Zaisa dalibi ya zama aboki ga mutanen da ba zai so a koda gansu tare ba idan komai yana tafiya dai dai. Bakanike, mai sai da katin waya, mai tallan jaridu, da "yan achaba na yankin sa zasu zama sune abokan sa.

Ku biyo mu a shafimu na Facebook a https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da kuma Tuwita a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel