A rage shan farfesun Kifi, Inji Masana

A rage shan farfesun Kifi, Inji Masana

– Masana sun yi gargadi game da cin kifin nan mai suna kurungu

– Cin kifin yana jawo cuta a jikin Dan Adam

– Kwararru sun kira ‘Yan Najeriya su rage amfani da kurungu a miya

A rage shan farfesun Kifi, Inji Masana
A rage shan farfesun Kifi, Inji Masana

Kwararru sun yi gargadi game da cin kifin nan da aka sani da suna kurungu, suka ce yawan cin san a kawo cuta a jikin Dan Adam. Wani Likita mai suna Dakta Arikawe Adeolu yake bayyana haka a Garin Abuja.

Babban Likitan da ke aiki a Asibitin Tarayya na Jabi da ke Abuja yake bayyanawa wajen wata hira da aka yi da shi cewa kifin nan kurungu yana da illa a jikin Mutum. Daktan yace kifin na dauke da wasu sinadarai da aka iya jawo kumburi a jika.

Dakta Adeolu yace kifin na iya jawo cutar hawan jini da ciwon sukari idan ba a bi a hankali ba. A Najeriya dai an saba shan farfesun irin wannan kifi. Akwai abin da ake kira fatty acid, wannan sinadari yana da tasari ga abin da ake kira kwalastaral.

KU KARANTA: Dubi Amaryar Sarkin Kano

A can Jihar Ekiti kuwa Yanzu haka har farfesun kare ake yi a wasu wuraren. Abin dai har ta kai babu karnuka a kan titi, don kuwa tuni sun shige tukunya.

Yanzu haka Karnuka sun fara bacewa a Jihar Ekiti, domin kuwa duk inda ka shiga cin abinci sai dai ka ga naman kare a cikin miya. Mutanen Jihar Ekiti dai sun komawa naman karnuka. Hukumar Dillacin labarai na Kasa ta bada wannan labara. Haka zalika, Sai dai masana sun ce naman kare yana da illa kwarai a jikin Dan Adam.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng