Mutumin daya auri mata biyu a rana daya yayi karin bayani

Mutumin daya auri mata biyu a rana daya yayi karin bayani

Idan ba’a manta ba a ranar Asabar 30 ga watan Disambar 2016 ne wani matashi a jihar Nassarawa ya auri mata biyu Kahdijah da Rashida a rana daya, lamarin daya daure ma jama’a kai.

Mutumin daya auri mata biyu a rana daya yayi karin bayani
Dahiru da Amarensa

Bayan cecekuce daya biyo bayan auren nasa, Malm Isiyaka Dahiru yayi bayanin dalilin daya sanya shi yanke shawarar auren mata biyu a rana daya.

Dahiru yace yana kaunar kowace mace a cikinsu sosai kuma daidai wa daida, sai dai wasu matsaloli daya samu a baya da matarsa ta fari ne ya sanya shi daukan wannan mataki.

KU KARANTA:Wani mutum mai shekara 30 ya aure mata biyu a rana daya (hotuna)

Lokacin da Dahiru ke yi ma jaridar Daily Nigerian bayani yace: “dama can muna soyayya da Rashida tun kafin na rabo da matata ta fari, burina shine na auri mata biyu. Amma bayan na rabu da matar tawa ta farko sai na hadu da Khadijah a wurin aikin mu, nan ma muka fara soyayya.

Dahiru da Amarensa
Mutumin daya auri mata biyu a rana daya yayi karin bayani

“akwai kyakkyawan fahimta tsakanin mu, suna girmama juna, har ma suna cin abinci tare. Ina kaunar su daidai-wa-daida, kuma nima ina samun kulawa daidai gwargwado daga wurinsu. Sun cika duk sharuddan da mace ya dace ta mallaka, don haka naga ba zan jure rashin aurensu gaba daya ba.”

Da aka tambaye shi ko zai kara aure a nan gaba, sai yace bai sani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: