Gwamnoni sun daina yin wayar tarho

Gwamnoni sun daina yin wayar tarho

– Sakamakon abin da ya faru da Gwamna Wike da Ayo Fayose, Gwamnoni sun shiga taitayin su

– Yanzu haka, Gwamnoni da dama sun daina waya a salula gudun tonon silili

– Gwamnonin sun komawa kafafe irin su Whatsapp da sauran su

Gwamnoni sun shiga taitayin su
Gwamnoni sun shiga taitayin su

Gwamnoni dai sun yi wa kan su karatun ta-natsu bayan ganin abin da ya faru da ‘Yan uwan su. Kwanan nan wani sabon sauti ya fito, inda aka ji Gwamna Fayose da Gwamna Wike suna murnar murde zaben Jihar Ribas da suka yi.

Jaridar Punch tace wannan dalili ya sa Gwamnoni da dama sun shiga taitayin su, sun kuwa daina magana ta wayar salula muddin dai abin da za a tattauna din ba karamin lamari bane. Hukumar DSS dai na daukar irin abin da Gwamnonin suka tattauna a wayar tarho.

KU KARANTA: CAN ba ta ji dadin shirun Shugaba Buhari ba

Gwamnonin dai sun komawa kafafen sadarwa na zamani na yanar gizo irin su whatsapp da facebook da abin da ake kira BBM domin isar da sakonnin su. Wasu daga cikin irin wadannan kafafe dai suna bada daman zance na sirri da kuma hana wani bare ya dakile ko ya ga sakon da aka aika.

A baya-bayan nan dai, an dai samu sautin wayar tarhon da ya wakana tsakanin shi Gwamna Fayose da takwaran sa, Wike na Jihar Ribas. Fayose yace wannan abin kunya ne ace ana amfani da Hukumar DSS domin dauko tattaunawar su. An ce dai wani Gwamna har ya nemi na’ura da ke bayyanawa mutum idan har ana leken sa. Wasu kuma sun komawa irin tsofaffin wayoyin nan na da.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel