Kyakkyawan sauyi na nan tafi a 2017 inji Shugaba Buhari

Kyakkyawan sauyi na nan tafi a 2017 inji Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yace duk wadanda suka fara gajiya da salon mulkin sa zasu ga sauyi a cikin shekara mai zuwa ta 2017, ta hanyar amfani da kudin da hukumar EFCC ta kwato daga wadanda aka samu da almundahana.

Kyakkyawan sauyi na nan tafi a 2017 inji Shugaba Buhari
Kyakkyawan sauyi na nan tafi a 2017 inji Shugaba Buhari

Shugaban wanda da alamu ya fahimci yadda mutane ke korafi kan tsadar rayuwa, ya nanata cewa bazai ci amanar mulki da masu zabe sama da Miliyan 15 suka daura masa ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayin ta game da shinkafar roba

Yace har yanzu ba a san iyakar kudin da aka sata zuwa kasashen waje ba, kuma kudin da aka samu aka kwato sune za a saka cikin kasafin kudi na shekara mai zuwa.

Sai dai wasu magoya bayan shugaban na ganin zai iya cimma nasara ne kawai ta hanyar shigar da ‘yan siyasa da ke kusa da al’umma cikin gwamnatinsa. Haka kuma dayawa daga cikin magoya bayan shugaban na ganin tamkar mota ta tashi ta barsu a tasha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel