Buhari zai yi wa mukarraban sa garambawul don kyautatawa Tinubu
Wasu rahotanni da ba'a tantance ba sun nuna shugaban kasa, Muhammadu Buhari na shirin sasanta rikicinsa da tsohon Gwamnan Lagos Bola Tinubu ta hanyar nada yaranshi mukamai.
Bayanai sun nuna shugaban kasar na shirye-shiryen yin garanbawul a majalisar Ministocinsa a inda ya dauko Uku daga cikin yaran Tinubu domin basu mukamai daban daban.
Mutanen dai sune :-
Dr Olusegun Abraham dan takarar Gwamnan Ondo wanda Tinubu ya marawa baya amma bai kai labari ba.
KU KARANTA KUMA: Kyakkyawan sauyi na nan tafi a 2017 inji Shugaba Buhari
Da kuma, Honourable James Faleke dan majalisar dokokin jihar Kogi wanda ya yaso zama Gwamnan Kogi bayan rasuwar mai gidansa suna dab da lashe zabe. Sai dai shima ya sha kashi a hannun Bello.
Sai kuma Mr Wale Edun tsohon kwamishinan kudi na jihar Logos a zamanin Gwamnatin Tinubu.
Majiyar mu ta ce, Dr Olusegun Abraham zai maye gurbin karamin ministan Niger Delta Farfesa Claudius Omoyele Daramola, wanda ake ganin ya gaza.
Sai Mista Faleke kuma majiyar ta ce shine zai maye gurbin ministan da ya mutu daga jihar Kogi margayi Ocholi.
A yayinda, Mista Edun zai maye gurbin Fashola, wanda Buhari ke shirin nadawa Sakataren Gwamnatin tarayya biyo bayan badakalar da ake zargin Babachir Lawal.
A sabuwar shekara ne dai ake tsammanin Shugaba Buhari zai yi garanbawul ga majalisar ministocin nasa a inda zai kara wasu sannan kuma zai sauke wasu daga ciki wadanda ake ganin basa tabuka komi.
Koma dai menene lokaci shi zai fayyace komi.
Asali: Legit.ng