An maka Gwamnatin Najeriya a Kotu

An maka Gwamnatin Najeriya a Kotu

– An kai karar gwamnatin tarayya kara Kotun Majalisar Dinkin Duniya

– Wata kungiya tace dole a kawo karshen rikicin Kudancin Kaduna

– Ana ta rikici a Yankin Kudancin Jihar tsakanin ‘Yan Gari da Makiyaya

An maka Gwamnatin Najeriya a Kotu
An maka Gwamnatin Najeriya a Kotu

Kungiyar SERAP mai zaman kan ta, ta maka Gwamnatin Kasar nan kara a Kotun Majalisar Dinkin Duniya watau UN game da abin da ke faruwa a Kudancin Jihar Kaduna. Har yanzu dai Gwamnatin Kasar tayi bakkam ba tace ko uffan ba.

Kungiyar ta SERPA tace dole a kawo karshen rashin rayuka da ake yi; musamman ma na kananan yara da mata a Yankin. Kawo yanzu dai an bada rahoton cewa mutane 800 suka rasa rayukan su a Yankin ga Makiyaya.

KU KARANTA: An kama Dan Boko Haram a Abuja

Shugaban Kungiyar, Adetokunbo Mumuni ya nemi Majalisar Dinkin Duniya; UN tayi bincike game da asalin abin da ya haddasa rikicin da kokarin magance sa. Kungiyar tace Gwamnati ta gaza wajen kawo karshen rikicin da ya jawo asara na rayuka fiye da dubu da biliyoyi na dukiya.

Kwanaki Mai Girma Gwamna Nasir El-Rufai yace ya fara tattaunawa wannan batu da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da kuma Ministan tsaro da ma Shugabannin Hafsun Soji. Ana sa ran kafa Gidan Rundunan Soji a Yankin Kauru da kuma Sanga na Jihar domin kawo karshen rikicin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel