Jerin makarantun da yayan Buhari suka yi karatu a kasashen waje
Duk da irin zantuttukan da ake dangantawa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na siyasa, amma shugaban bai yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da yayansa sun samu karatu ingantacce kamar yadda kamata.
![Jerin makarantun da yayan Buhari suka yi karatu a kasashen waje Jerin makarantun da yayan Buhari suka yi karatu a kasashen waje](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt1dmmqld7qcto.jpeg?v=1)
Cikin wani sharhi da jaridar Premium Times tayi ma littafin tarihin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda wani bature farfesa John Paden ya wallafa “Muhammadu Buhari: The Challenges of Leadership in Nigeria” an gano makarantun da yayan shugaba Buhari suka je, dukkansu,
1- Fatima: An haifi Fatima a shekarar 1975, inda tayi karatun ta a makarantar firamaren sojojin sama dake tsibirin Victoria jihar Legas, sa’annan tayi sakandaren kwalejin gwamnati dake Kaduna, sait wuce jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda ta yi karatun gaba da digiri a cibiyar kasuwanci dake Stratford, kasar Birtaniya.
KU KARANTA:Buhari ne gwani na – Inji shugaban kasar Guinea Bissau
2- Nana Hadiza: an haifi Hadiza a ranar 23 ga watan Yuli na shekarar 1981, inda tayi karatuttkanta a Essence International School dake Kaduna; Cobham Hall, Kent, United Kingdom; jami’ar Buckingham dake Birtaniya; sai cibiyar koyar da malamai ta Kaduna, sa’annan ta kara da digiri na biyu a fannin sanin alakar kasashe, kuma ta yi karatu a kwalejin kimiyya da fasaha na Kaduna.
3- Safinatu: An haife ta a ranar 13 ga watan Oktoba inda tayi karatuttkanta a Essence International School dake Kaduna; Cobham Hall, Kent, United Kingdom; jami’ar Plymouth dake Birtaniya, a yanzu kuma tana jami’ar Arden duk a kasar Birtaniya.
4- Halima: Halima itace babbar yarinyar Aisha Buhari, wanda aka haifeta a ranar 8 ga watan Oktoba 1990, tayi karatu a International School, Kaduna; sakandaren British School dake Lome, Togo; kwalejin Bellerby dake Brighton,kasar Ingila; sai jami’ar Leicester dake Ingila , sai kuma makarantar horar da lauyoyi dake Lagos.
5- Yusuf Buhari: Yusuf Buhari yayi karatu a a International School, Kaduna; sakandaren British School dake Lome, Togo; kwalejin Bellerby dake Brighton,kasar Ingila sai ya tafi jami’ar Surrey a Ingila.
6- Zahra: an haifi Zarah a 1994, 18 ga watan Disamba, tayi karatu a International School, Kaduna; sakandaren British School dake Lome, Togo; kwalejin Bellerby dake Brighton,kasar Ingila sai ta tafi jami’ar Surrey a Ingila.
7- Aisha (Hanan): An haife ta a ranar 30 ga watan Agusta 1998, tayi karatu a Kaduna International School.
8- Noor (Amina): AN haife ta a ranar 14 ga watan Satumba 2004, a yanzu tana karatu a Kaduna International School.
Idan ba’a manta ba a shekarar 2012 ne babban yarinyar shugaba Buhari ta rasu, Zulaihat sanadiyyar ciwon sickler. A baya ma an taba samun yaron shugaba Buhari Musa daya rasu tun yana jariri.
Zaku iya samun labaran mu a nan ko a nan.
Asali: Legit.ng