Abin Al’ajabi: An haifi wani Jariri ba hanci

Abin Al’ajabi: An haifi wani Jariri ba hanci

A wasu lokuta da dama Allah ya kan yi wasu halittun ban mamaki da al’ajabi domin su zamo izina ga mutane, ko mutane zasu yi ma Allah godiya.

Abin Al’ajabi: An haifi wani Jariri ba hanci

An samu wani jariri a garin Alabama na jihar Amurka wanda aka haifa ba tare da hanci ba, sunansa Eli.

Lamarin Eli ya daure ma su kansu likitocin da suka karbi haihuwarsa kai, kamar yadda mahaifiyar jaririn Brandi Mc Glathery ta cika da mamakin irin halittar Eli.

Abin Al’ajabi: An haifi wani Jariri ba hanci

KU KARANTA:Ba maraya sai rago: Kalli yadda guragu ke neman kudi

Masana sun yi bayanin halittar Eli da sun a ‘Arrinia’ ko kuma ace masa ‘Congential Arrinia’ wanda suka ce ana samunsa ne a kan mutum 1 cikin duk mutane miliyan 197.

Abin Al’ajabi: An haifi wani Jariri ba hanci

Likitoci sun ce matsalar Eli guda ce, rashin hanci, amma yana da duk sauran halittan shaker iska da suka danganci hanci. Sai dai sunce zasu cigaba da yi mai tiyata lokaci zuwa lokaci don ya dinga samun saukin shaker iska ta makwagoronsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng