Boko Haram: Yadda muke lalata da ‘yan mata kamammu

Boko Haram: Yadda muke lalata da ‘yan mata kamammu

-Wani yaro 15 da Boko Haram suka tilasatawa aikin soja ya bayyana yadda suke ake sa su lalalata mata kamammu

-Yaron wanda 'yan Boko Haram su ka sace a Baga, Najeriya ya bayyana yadda manyan mayakan koya musu yadda za su afkawa 'yan matan da su ke tsare da su

Boko Haram: Yadda muke lalata da ‘yan mata kamammu
Boko Haram na tilasta yara lalata da mata kamammu a cewar wani da ya tsere daga hannunsu

Wani yaro dan shekara 15 wanda ‘yan Boko Haram suka sace, suka kuma tilastawa aikin soja ya bayyana yadda ake su lalata da matan da kamammu.

A cewar yaron mai suna Ahmad, wanda kuma ya tsere daga wajen mayakan, ya ce, manya daga cikin su kan gaya wa matasan cewa za su samu nishadi wajen lalata kamammun.

An rawaito 'yan ta'addan na kara shigar da yara cikin rundunarsu don kara karfi tunda su ka yi mummunar asarar mutanensu a yakin da su ke da sojin Najeriya.

Yaron da 'yan Boko Haram su ka sace a Baga, Najeriya ya bayyana yadda manyan mayakan ke shafe kwana biyu suna koyar da yara yadda za su afkawa 'yan matan da su ke tsare da su.

Ya ce a na koyar da yara maza su murkushe abokan fadansu kuma kar su sake su bar mata su fi karfin su. Jaridar Daily Post ta kuma rawaito cewa,

"Yan matan za su yi karaji da kuka su na neman taimako amma ba ruwansu. Wasu lokutan a mare su, a yi ma wasu barazana da bindiga in ba su bayar da hadin kai ba."

Wata yarinya da ta kubuto daga hannun Boko Haram ta zayyana yadda 'kananan yara' su ka lalata ta, yaran da a zahiri za ta iya gamawa da su cikin sauki.

A wani makamancin ci gaban, rundunar sojin Najeriya ta fitar da hotunan bidiyo da ke nuna farmakin sojojin a sansanin Boko Haram na karshe da ke cikin makeken dajin Sambisa, wanda ya kasance babbar mafakar Boko Haram tsawon shekaru.

Fefen ya nuna 'yan ta'addan na Boko Haram na tserewa daga Camp Zero biyo bayan rubdugun bamabamai da sojin su ka yi wa sansanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng