Mataimaki gwamna ya gina Masallacin Juma’a a jihar Adamawa

Mataimaki gwamna ya gina Masallacin Juma’a a jihar Adamawa

Mataimakin gwamnan jihar Adamawa Martins Babale ya gina ma al’ummar musulmai babban masallacin Juma’a a garin Dalasum dake karamar hukumar Toungo.

Mataimaki gwamna ya gina Masallacin Juma’a a jihar Adamawa
Martins Babale

Rahoton kamfanin dillancin labarai (NAN) ya bayyana cewar Babale ya mika ma musulman garin masallacin a ranar 28 ga watan Disamba. Babale wanda Kirista ne yace dalilinsa na gina masallacin shine don karfafa dangantaka tsakanin addinan yankin daban daban.

KU KARANTA: ‘Yan Shi’a sun yi Bikin Kirismeti tare da Kirista

Sa’annan ya jaddada cewar zamanin fadace fadacen addini d kabilanci tsakanin mabiya addinai daban daban ya wuce, inda ya bukaci jama’a da su zauna lafiya da junansu. Babale yace: “a yau ina cika ma mutane na alkawarin dana daukan musu, ina fata masallacin ya zamo cibiyar hadin kan al’ummar yankin nan.”

Yayin dayake mayar da martani, hakimin Dalasum Alhaji Musa Gindau, ya yaba ma mataimakin gwamnan, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai son cigaban zaman lafiya. Gindau yace al’ummar garin Dalasum mutane ne masu zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da banbancin addini ko na kabila.

Shima shugaban karamar hukumar, Ustaz Abubakar Garba ya bukaci jama’an dasu cigaba da zaman lafiya da juna tare da girmama junansu. Garba yace wannan zai kara hada kan mutanen yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng