Naman Kare ya zama Kifi a Ekiti

Naman Kare ya zama Kifi a Ekiti

– Jama’a sun komawa naman kare a Jihar Ekiti

– Duk inda ka je kurum da naman kare ake dagargajewa

– Ana sayar da jariran karnuka har N500

Yanzu haka Karnuka sun fara bacewa a Jihar Ekiti, domin kuwa duk inda ka shiga cin abinci sai dai ka ga naman kare a cikin miya. Mutanen Jihar Ekiti dai sun komawa naman karnuka. Hukumar Dillacin labarai na Kasa ta bada wannan labara.

A Garuruwa irin su Ise-Ekiti, Ado-Ekiti, Ikere-Ekiti da sauran su naman Karen ya zama wani kayan Gabas, ko ina rububin kare ake yi. A gidaje da wuraren cin abinci ma da Gidan ruwa, ko ina kare kurum ake babbakawa ba kama hannun yaro.

KU KARANTA: Jami'an kwana-kwana sun ceto wata Yarinya

Yanzu haka har farfesun kare ake yi a wasu wuraren. Abin dai har ta kai babu karnuka a kan titi, don kuwa tuni sun shige tukunya. A na sayar da jariran karnuka a kan N500, manya kuma su kan kai har N15000; ain dai, iya kudin ka, iya shagalin ka.

A watan Agusta Gwamna Fayose na Jihar ya sa hannu kan wata doka da ta haramta kiwon shanu da sauran dabbobin noma a Jihar, Dokar tace duk wanda aka kama ya saba doka, za a daure sa na rabin shekaru kuma babu damar karbar tara. Dokar ta haramta kiwo daga karfe 6 na yamma har zuwa 7 na safe. Sai dai masana sun ce naman kare yana da illa kwarai a jikin Dan Adam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng