Tsohon Gwamnan Delta Uduaghan ya gargadi magoya bayan Ibori

Tsohon Gwamnan Delta Uduaghan ya gargadi magoya bayan Ibori

Dakta Emmanuel Uduagan, tsohon gwamnan jihar Delta ya ja kunnen magoya bayan wanda ya gaji mulki a wajensa, James Ibori kada su jawowa shi Iborin karin matsaloli ta hanyar murnar da su ke yi kan fitowar sa daga gidan yari.

Tsohon Gwamnan Delta Uduaghan ya gargadi magoya bayan Ibori
Tsohon gwamna James Ibori da wasu magoya bayansa da suka je tararsa daga gidan yari a Landan

Da yake magana da jaridar The Nation, Udaghan ya nuna damuwarsa cewa, abubuwan da magoya bayan Iborin ke yi ka iya tsunduma shi cikin karin wasu rigingimun siyasa.

Tun fitowarsa daga gidan yari inda ya shafe shekaru 13 kan laifuffukan da su ka danganci almundahana da cin hanci a satin da ya gabata, gidansa tsohon gwamnan James Ibori da ke London ya zama dandalin ziyarar ‘yan siyasar jihar.

Cif Monday Igbuya, kakakin majalisar dokokin jihar kuma jigo a jam'iyyar PDP, Cif Ighoyota Amori na daga cikin wadanda su ka ziyaci Ibori.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon gwamna Udaghan ya ce:

"Wadanda su ke zuwa London su ziyarci Ibori su na saka hotuna da jawabai, to ku daina.

"Mu na jin dadin soyayyar ku gare shi. Amma za ku iya zuwa salin alin ba tare da kwarzanta wa ba. Ku na kara kirkirar matsaloli gare shi fiye da tsammanin ku.

"Najeriya kasa ce mai wuyar sha'ani kuma dole ku fahimta ku kuma mutunta tunanin mutane."

A wani ci gaban mai kama da wannan, a wani hoton bidiyo da ya ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, sanata Peter Nwaoboshi ya ce Ibori ya yi sanadiyyar gwamnoni kamar gwamna mai ci Ifeanyi Okowa da sanatoci kai har ma 'yarsa Eriatake Ibori ya sa ta zama 'yar majalisar jiha da sauransu.

Ibori wanda ya kasance gwamnan jihar mai arzikin man fetur tsakanin shekarun 1999 da 2007, ya fito daga gidan yarin Ingila a ranar Laraba 21 ga watan Disamba bayan shafe shekaru 13 kan almundahanar kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: