‘Yan Shi’a sun yi Bikin Kirismeti tare da Kirista
– ‘Yan Shi’a sun yi Bikin Kirismeti tare da Kirista
– An ga Mabiya Shi’a a Coci tare da Kiristoci suna taya su murna
– Mabiya Shi’a sun kuma aika katin taya murna ga Kirisoci
‘Yan Shi’a sun taya Kiristoci murnar Bikin Kirismeti wannan shekarar a Garin Kaduna. An dai ga Mabiya Shi’a da dama a cikin Coci tare da Kiristooci yayin da ake Bikin Kirsmetin wannan shekara.
Har da wani kati kuma ‘Yan Kungiyar IMN ta Shi’a ta aika domin taya Kiristoci murnar wannan Idi. A kan yi Bikin Kirismeti na a Ranar 25 ga Watan Disamba da cewa a Ranar ne aka haifi Yesu.
KU KARANTA: Shugaba Buhari zai yi girgiza
A Kasashe irin su Iran, tuni dama an dade ‘Yan Shi’a suna shiga Coci domin su taya Kiristoci Kirismeti. Sai ga shi wannan abu ya faru wannan karo a Garin Kaduna, hakan dai y aba kowa mamaki.
A baya dai Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa daga yanzu babu wani tattaki ko gangamin da ya sabawa doka a Jihar. Gwamnatin tayi wannan ne domin kawo karshen lamarin ‘Yan Kungiyar IMN na Shi’a a Yankin da ta kira masu tada zaune tsaye.
Asali: Legit.ng