Janar Buratai yayi kalaci tare da Sojoji a dajin Sambisa

Janar Buratai yayi kalaci tare da Sojoji a dajin Sambisa

Babban hafsan sojan kasa, Laftanr Tukur Buratai ya kai ma sojojin sa dake filin daga ziyara bayan sun samu nasarar fatattakar yayan kungiyar Boko Haram daga dajin Sambisa.

Janar Buratai yayi kalaci tare da Sojoji a dajin Sambisa

Janar Buratai ya kai ziyarar ne don kara ma sojojin gwiwa tare da yi musu godiya, sa’annan har ma yayi kalaci tare da sojojin.

KU KARANTA: Sojoji na cin bakar wuya a Sambisa

Shima shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba ma mayakan rundunar sojan kasa bayan sun samu nasarar, sa’annan ya jinjina musu saboda jarumtar da suka nuna:

Janar Buratai yayi kalaci tare da Sojoji a dajin Sambisa
Janar Buratai yayi kalaci tare da Sojoji a dajin Sambisa
Janar Buratai yayi kalaci tare da Sojoji a dajin Sambisa

Shugaba Buhari yace “ina mai matukar farin ciki samun labarin yadda dakarun mu suka kwato dajin Sambisa, ina so nayi amfani da wannan dama in yaba ma sojojin mu a bisa dagiya, juriya da kware da suka nuna, tare da dagewarsa wajen kakkabe sauran mayakan Boko Haram a mabuyarsa dake tsakiyar dajin Sambisa.

“Babban hafsan askarawar sojan kasa ya shaida min cewar da misalin karfe 1:35 na ranar Juma’a 22 ga watan Disamba ne aka fatattaki yayan Boko Haram daga dajin Sambisa, a yanzu haka mun san basu da wajen boyewa kuma, don haka nake son mu bi su duk inda suke mu kama su

“da wannan ne nake yin kira ga yan Najeriya dasu baiwa rundunar sojan kasa hadin kai da sauran hukumomin tsaro ta hanyar bayar da ingantaccen rahoton da zai basu daman gano duk inda wani dan Boko Haram yake.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng