Kundin Kannywood: Ina son aure - inji Hadiza Gabon

Kundin Kannywood: Ina son aure - inji Hadiza Gabon

Shahararriyar 'yar fim din Kannywood din nan, Hadiza Gabon, ta ce tana so ta yi aure amma lokaci ne kawai bai yi ba.

Da take hira da majiyar mu, Hadiza ta ce aure lokaci ne, kuma kamar mutuwa, idan Allah ya kawo shi babu yadda mutum zai guje masa.

Kundin Kannywood: Ina son aure inji -Hadiza Gabon
Kundin Kannywood: Ina son aure inji -Hadiza Gabon

"Wallahi babu wata mace da za ta so ta kai lokacin aure amma ta ki yi" inji Gabon.

Jarumar, wacce ta lashe kyautar 'yar wasan da ta fi tallafawa babban jarumi a fim ta Africa Films Awards na bana, ta ce tana kaunar duk masu goyon bayanta.

Hadiza Gabon, ta ce babu wacce za ta so ta rinka kaiwa-tana-komowa a gaban iyayenta ba tare da ta yi aure ba, alhalin kuma ta kai munzalin yin hakan.

A hirar da majiyar mu ta yi da ita da kuma Ali Nuhu, jarumar ta yi kira ga masu kaunarta da su yi mata addu'a.

Ta kara da cewa duk wata 'yar fim "da ka gani, to wallahi tana so ta yi aure".

Muna so mu yi, amma babu yadda muka iya saboda ba za mu auri kanmu ba.

"A don haka addu'a muke nema daga wurinku," a cewarta.

Ana sa bangaren Ali Nuhu ya yaba yadda jarumar ta koyi harshen Hausa da Turanci, da kuma irin rawar da take takawa a fim.

Ku biyo mu a tuwita @naijcomhausa ko shafin Facebook Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel