Mata a zindir sunyi zanga-zangar kin jinin gwamnatin El-Rufa'i (Hotuna)

Mata a zindir sunyi zanga-zangar kin jinin gwamnatin El-Rufa'i (Hotuna)

Wasu fusatattun mata sun yi zanga-zanga tsirara a yankin Kudancin Kaduna, kwana daya bayan wani rikici da aka yi a Kafanchan.

Mutane da dama aka kashe sakamakon rikicin da ya barke lokacin da matasan yankin suka yi wata zanga-zanga a ranar Litinin.

Mata a zindir sunyi zanga-zangar kin jinin gwamnatin Elrufa'i (Hotuna)
Mata a zindir sunyi zanga-zangar kin jinin gwamnatin Elrufa'i (Hotuna)

Matan sun yi zanga-zangar ne yayin da tawagar gwamnan jihar Malam Nasir El-rufa'i ta kai ziyara yankin, don ganin irin ta'adin da aka yi.

Fisatattun sun kuma farfasa motocin tawagar gwamnan sakamakon jefe-jefe da suka ringa yi da duwatsu.

Masu zanga-zangar dai sun fito ne duk kuwa da dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 da aka ayyana, inda suka ce sun gaji da kashe-kashen mutane da ake yi a yankin.

Mata a zindir sunyi zanga-zangar kin jinin gwamnatin Elrufa'i (Hotuna)
Mata a zindir sunyi zanga-zangar kin jinin gwamnatin Elrufa'i (Hotuna)

Tun da farko dai, gwamnan jihar ta Kaduna ya yi wa matan jawabi, sannan ya kuma amsa tambayoyinsu.

Wakilin majiyar mu da ke cikin tawagar ya ce zanga-zanagr matan tsirara ta kunyata duka mutanen da suka halarci wajen.

Gwamna El-rufa'i ya shaida wa matan an kara daukar matakan tsaro domin kawo karshen rikici a yankin.

Wakilinmu ya ce an yi ta'adi sosai yayin zanga-zangar da aka yi ranar Litinin wacce ta rikide zuwa kone-konen wurare, ciki har da masallatai da kuma coci-coci.

Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa

Ku biyo a shafin fezbuk: Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: