Dan shekara 100 yayi lalata da karamar yarinya

Dan shekara 100 yayi lalata da karamar yarinya

– Wani tsohon mai fiye da shekaru 100 a duniya zai yi zaman kaso

– Za a daure wannan tsoho na shekaru 13 a gidan maza

– An kama wannan tsoho da laifuffuka sama da 21

An kama wani Tsoho gota-gotai da shi da lafin daurin na shekara da shekaru. Yanzu haka dai za a daure wannan tsoho mai sama da shekaru 101 na shekaru 13 a Gidan Yari a Kasar Birtaniya.

Duk Kasar Birtaniya da wuya a samu Tsohon da zai shiga Gidan Maza sa’ar wannan mutumi da ya ba shekaru 100 baya. Kotun da ke Birmingham ta kama wannna tsoho da laifuffuka sama da 21. Sunan wannan mutumi Raplph Clarks.

KU KARANTA: Manyan Labarai a Najeriya

An kama wannan mutumi da laifin yin lalata da yara kanana masu shekaru 5 zuwa 13 a wancan lokaci. Wadanda abin ya auku gare su, sun tsufa yanzu, don sun kere shekaru 40. Sai dai Tsohon yace karya ake yi masa kurum.

Wani yaro dai ya bayyana cewa tabbas Tsohon yayi lalata da shi loakcin baya. Yaron ya bayyanawa Kotu ne hakikanin yadda abin yake. Tsohon ya kasance yana tuka Gingimari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng