Kare ya kashe wani jinjiri

Kare ya kashe wani jinjiri

– Ashe dama kare na cin mutum?

– Wani kare ya cinye wani jinjiri da aka jefar a bola

– Wannan abin al’ajabi ya faru ne a Jihar Bauchi

Kare ya kashe wani jinjiri
Kare ya kashe wani jinjiri

Wani abin ban mamaki matuka ya faru a Garin Bauchi a cikin kwanan nan. Wani kare ne dai ya cinye wani jinjiri. Ashe ko dama kare na cin mutum?

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an samu wani kare yana cin wani jinjiri da aka jefar a bola a Garin Gwallameji na Jihar Bauchi. Wannan abu ya faru ne a wajen Makarantar Polytechnic da ke Jihar Bauchi.

Wasu ne dai suka jefar da jinjiri a bolar da ke wurin. Sai dai aka ga kurum kare ya sa baki yana cinye wannan jariri. Mutane da dama sun ga wannan abu mai ban al’ajabi. Wani mai suna Isiah yace ya dawo Coci kenan ya ga jama’a an taru, ko da ya samu zuwa inda aka taru sai ya ga abin da yake faruwa. Yace abin duk kyama, ya iske kare yana cin jaririn da aka jefar.

Mutane dai sun ce an jefar da yaron ne da ran sa, sai dai wannan karen ne ya kashe sa. Wannan abin dai bai yi wa kowa dadi ba. Mutane dai sun haka rami ne inda suka bizne gawar wannan jinjiri.

Mai Garin Gwallameji ya bayyanawa ‘yan jarida cewa ba ya wajen sa’ilin da abin ya faru amma ya samu labarin abin da ya auku. Ba dai yawa bane farau da aka samu an jefar da jariri a wannan yankin ko ma Kasar ta mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng