Yaro ya ƙera jirgin sama mai tashin Angulu a jihar

Yaro ya ƙera jirgin sama mai tashin Angulu a jihar

Sanin kowa ne cewa mu a Legit.ng mun shige gaba musamman wajen bayyana ma Duniya tarin hazikan mutanen yan Najeriya masu basira daban daban.

Idan za’a iya tunawa, a baya mun kawo muku rahoton wani yaro Agoucha Chinwedum daya kera mota a jihar Imo, A yanzu ma mun kawo muku labarin wani yaro daya kera jirgin sama mai tashin Angulu, wanda wani ma’abocin kafar sadarwa ya dauko rahotonsa tare da hotunan yaron da na jirgin daya kera.

KU KARANTA:Hukumar Soji ta gargadi jami’anta dake amsan na goro a hannun direbobi

Ga wasu daga cikin hotunan jirgin:

Yaro ya ƙera jirgin sama mai tashin Angulu a jihar

Yaro ya ƙera jirgin sama mai tashin Angulu a jihar
Yaro ya ƙera jirgin sama mai tashin Angulu a jihar

Ga yadda majiyar mu ta dauko rahoton:

“A daidai lokacin da muke murna da kamfanin INNOSON, sai ga wani karamin yaro daga garin Owerri ya kera jirgin sama mai tashin Angulu.”

Labarin yaron mai suna Alex Ephraim ya bayyana yadda idan mutum ya dage kan abinda yake so, zai iya samu, sa’nnan wannan ya kasance kalubale ga sauran yara, musamman kanikawa dasu dage su kera wani abu da zai amfani mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: