Wata mata ta saka hoton ta cikin hotunan auran Zahra Buhari

Wata mata ta saka hoton ta cikin hotunan auran Zahra Buhari

- Hotunan wata mata yar arewa a cikin hotunan auran Zahra Buhari yayi zagaye yanar gizo cikin sauri

- Matar wacce ta so kasancewa a bikin amma bata samu katin ya gayyata ba don haka ta yi amfani da fasaha

- A cikin hotunan, cikin hikima ta shuka kanta cikin hotunan auransu da taimakaon photo shop kuma ya kasance abun ban dariya.

Wata mata ta saka hoton ta cikin hotunan auran Zahra Buhari
Wata mata ta saka hoton ta a kofar shiga filin taron auran Zahra Buhari

Bikin yar shuaban kasar ya cika da manyan masu fada a ji a kasar. Ba wai kowa bane zai iya samun katin ayyata cikin sauki kamar yadda shugaban kasa ya so auran ya kasance a saukake.

Ga wadanda suka so kasancewa a gurin taron bikin don taya ma’auratan farin ciki, ya karya masu zuciya saboda basu samu damar kasancewa da Zahra ba a wannan rana ta musamman.

Don haka ne wannan matashiya ta yi amfani da damarta. Ya nuna karara cewa ta so kasancewa a gurin bikin don hakan ne ya kai ta ga amfanifasaharta gurin hada hotonta cikin hotunan ma’auratan da yayi fice. Kalli hotunan a kasa:

Wata mata ta saka hoton ta cikin hotunan auran Zahra Buhari
Matar tsaye a gefen hoton bikinsu
Matar sanye da wani kaya cikin hotunan bikin nasu
Matar sanye da wani kaya cikin hotunan bikin nasu

Don haka, wanene zai ce bata halarci bikin ba? Bayan tana da hujja na kasancewa a gefensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel