An kashe wani dan acaba a Ondo

An kashe wani dan acaba a Ondo

An kame wasu abokai biyu bisa zargin kisan wani acaba Wadanda ake zargi sun hallaka dan acaban ne a kokarinsu na kwace masa babur.

An kashe wani dan acaba a Ondo
An kashe wani dan acaba a Ondo

A cewar jaridar The Nation, rundunar ‘yan sandan jihar Ondo sun kame wasu abokai biyu a bisa zargin hallaka wani Thomas Amusan mai sana’ar baburin haya, wanda aka fi sani da Okada ko Acaba a Ile-Oluji a yankin Oke Igbo na jihar Ondo.

KU KARANTA KUMA: Uwargidan gwamnan jihar Kogi ta je duba yara masu illa a Abuja (hotuna)

Mai magana da bakin rundunar ‘yan sanda jihar Femi Joseph, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa, Rilwan Rasheed da kuma Sheu Akande wadanda suke tsare su a bisa zargin aikata kisan, ‘yan sandan sun damke su ne a ranar 8 ga wannan watan. Kakakkin rundunar ‘yan sandan ya ce, wadanda ake zargi Rasheed da kuma Akande, sun nemi marigayin ya kai su wani kauye a yankin, inda a kan hanyar zuwa suka hallaka shi, suka kuma tsere da babur din sa.

Bayan da rundunar ‘yan sandan suka samu labari ne, da taimakon bayanan sirri, suka yi nasarar damke wadanda ake zargi, a cewar rahoton jaridaSatar Babura tare da hallaka masu shi, na nema ya zama ruwan dare a wasu jihohin kasar, a inda a jihar Kano ma wasu ke daukar hayar masu babur mai kafa uku da ake kira a daidaita, zuwa wasu wurare su kuma hallaka su, su gudu da abin hawan nasu a cewar rahotanni.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel