Yadda wata tsohuwa tayi mini sane – Wata budurwa

Yadda wata tsohuwa tayi mini sane – Wata budurwa

Ubangiji yayi mata gyaar doguwa kuma “na je kasuwa a legas mislain karfe 2:30 na rana”

Yadda wata tsohuwa tayi mini sane – Wata budurwa
Yadda wata tsohuwa tayi mini sane – Wata budurwa

Wata budurwa mai suna Elle, ta gauraya shafinta na Instagram inda ta bayyana yadda wata tsohuwa tayi mata sane a Legas, ranan Laraba, 14 ga watan Disamba.

Elle wacce ta je siyyayan shirin kirismeti taga abiin mamaki a kasuwa, tace :

KU KARANTA: Dan Najeriya mai digiri 11

“Na je kasuwa a legas mislain karfe 2:30 na rana. Ina bukatan siyyaya. Da na kai wurin,wata mata ta dinga bina. Take ce mini, yarinya, ajiye kudinki da kyau. Na Legas ne, akwai barayi ko ina,”sai nace nagode mama. Sai ta kara ce mini in rike kudin a hannu saboda idan ma an kwace jakan a hannu na, inada wasu kudi a hannu. Sai na ciro kudaden a jaka na rikesu a hannun na,harda bani leda in sanya su.

“Yayin yin hakan, sai ta canz kudina. Ta sanya takardu cikin leda,ta bani ledan ta dauke kudina. Har ina cewa Nagoda mama… ashe ta kwashe mini kudi, kawai sai na fara mata wani kallo, sai ta fito da kudi cikin kayan ta. Sai na wuce shagon kwata inda na duba ledan da ta bani naga takardun jarida ne kawai a ciki. Yan uwana, ku kasance cikin farga . Nagode wa Ubangiji.”

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa, https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng