Messi ya faranta ma wani yaro dan kasar Afghanistan rai
Wani yaro da a kwanakin baya yayi suna bayan hotunan sa yana sanye da rigar leda ta Messi sun watsu a yanar gizo ya samu haduwa da Messi.
Messi tare da yaron mai suna Murtaza Ahmadi dan kasar Afghanistan ya hadu a garin Doha babban birnin Qatar inda kungiyar Barcelona zata fafata a wasan sada zumunta da kungiyar Al-Ahli, inji jami’an hukumar kwallon kafa ta Qatar.
KU KARANTA:An azabtar da kananan yara biyu kan zargin maita
Idan ba’a manta ba kafin haduwar tasu, shahararren dan wasa Lionel Messi ya aika ma Murtaza asalin rigar kwallonsa wadda take dauke da sa-hannun sa a kan ta, wanda aka aika ma yaron har gida.
Messi ya bayyana cewar zai dauko yaron a matsayin dan rakiyarsa a wasan sada zumuntan da za’a buga a ranar Talata 13 ga watan Disamba.
Sai dai a yanzu yaron dan asalin lardin Jaghori dake yankin Ghazni na kasar Afghanistan ya gudu daga kasar, inda ya koma kasar Pakistan tare da iyayensa sakamakon karuwar barazana da matsalar tsaro keyi musu.
Za'a iya bibiyan labaran mu a nan ko a nan
Asali: Legit.ng