Manyan labarai da suka girgiza Najeriya
Jaridar Legit.ng ta tattaro muku muhimman labarai da sukayi kani a jiya Talata ,13 ga watan Disamba.
1. Ban taba amsan albashi ba a matsayin gwamna - Aregbesola
Gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola yace bai taba amsan albashi ba a mastayin gwamna tun lokacin da ya dau ragamar mulki shekaru 6 da suka wuce.
2. Za’a cigaba da gurfanar na Nnamdi Kanu yau
Shugaban kungiyan Indigenous People of Biafra (IPOB) Mazi Nnamdi Kanu,ya cigaba da gurfana a babban kotun tarayya a Abuja. Magoya bayansa suna adduán samun nasaran Kanu a babban kotun tarayyan a yau 13 ga watan Disamba.
3. Abin kunya: Justice Ademola na gudun yan jarida a kotu
Kotu ta yanke hukuncin cewa Jastis Ademola zai bada belin kudin N50million. Duk dacewa Alkali mai shariar ya wajabta ma Ademola ya sallamar da dukkan takardun tafiyarsa ga magatakardan kotun,baá wajabta masa ajiye jingina ba.
4. Kotu ta yanke hukunci kan Nnamdi Kanu
Magoya bayan Kanu wadanda suka halarci gurfanar daga sassan yankin kudu maso gabas da dama sun cika kotu yau,suna addu’an. Game da rahoton Radio Biafra, jamian DSS da yan snada sun cika harabar kotun tabbatar da cewa babu wanda zai ketare kofar shiga kotun.
5. Akalla mutane 13 sun hallaka a hadari a jihar Katsina
Hukumar tabbatar da tsaron hanyar mota ta bada rahoton cewa akalla mutane 13 sun rasa rayukansu a wata mumunan hadari da ya faru a yau Talata, 13 ga watan Disamba a jihar Katsina.
6. Daskarewan MMM: Babu abinda za mu iya yi - EFCC
Dan sa ran da yan Najeriya key i akan daskarewan asusun masu hannun jari a bankin MMM wanda wani dan kasan Rasha a kaddamar ya ja baya,yayinda hukumar yaki da almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC tace babu abinda zata ita yi.
Ku kasance tare da mu: https://www.facebook.com/naijcomhausa, https://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng