Ali Modu Sheriff ya aurar da diya
– Shugaban bangaren PDP, Ali Modu Sheriff ya aurar da diyar sa a karshen wannan makon
– Manyan mutane da dama sun halarci wannan taron
– Da alamu kuma auren Diyar Shugaba Muhammadu Buhari, Zahra ya matso kusa
Tsohon gwamnan jihar Borno, kuma Shugaban bangaren PDP, Alhaji Ali Modu Sheriff ya aurar da diyar sa wannan makon da ya wuce. Diyar Tsohon Gwamnan, Halima ta auri wani Soja ne mai suna Ronnie Kabo.
Ronnie Kabo dai matashi ne, da bai wuce shekara talatin ba. Angon Kyaftin din Soji ne, kuma shine Dogarin Shugaban Hafsun Sojin Kasar, ya shiga daga ciki tare da tsaleliyar Amaryar sa Halima Ali Sheriff. Halima tayi karatu a Dubai, kuma ta kware a harkar kwalliya. Manyan ‘Yan Siyasan Najeriya sun halarci wannan taro.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya halarci wannan taro. Haka kuma Baba Shehuri; wanda yake Minista a yanzu. Tsofaffin Gwamnoni irin su Sule Lamido da Ibrahim Shekarau, da kuma Babangida Aliyu duk sun samu zuwa daurin auren.
Muna kuma samun kishin-kishin din cewa an sa Ranar auren Zahra Buhari; za a daura auren diyar Shugaban Kasar ne a Ranar 16 ga wannan wata, a Babban Masallacin Abuja, bayan Sallar Jumu’a. Zahra Buhari za ta auri Ahmed Muhammad Indimi.
Asali: Legit.ng