Girman Najeriya yayi yawa -Buhari

Girman Najeriya yayi yawa -Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce saboda girma ta fuskar yawa da kuma yawan mutane dama ma'adanai yakan sa duniya yi wa Najeriya din wani irin kallo na kasar da ya kamata ace tayi zarra a ta kowane irin fanni.

A cewar sa, kowa a duniya idon sa na akan kasar ta Najeriya don a tunanin su bai kamata ace anfi su yin zarra a wani bangare ba na rayuwa duba da yadda suke da hazikan mutane dama arzikin kasa.

Girman Najeriya yayi yawa -Buhari
Girman Najeriya yayi yawa -Buhari

Shugaba Buhari yayi wannan furuci ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu matasa masu wasan iyo na ruwa a fadar sa dake a Aso Rock villa wanda Sanata Kabiru Gaya ya jagoranta.

Shugaba Buhari sai ya bukaci matasan da su maida hankali wajen ganin sun jayo sauran matasan kasar nan wajen wasanni irin wadannan sannan kuma su dage suga sun lashe gasar don su kara daga kimar kasar.

A nashin bangaren jagoran tawagar Sanata Gaya ya bayyana cewa makasu din kungiyar matasan shine don ya habaka wasannin iyo din tare da zakulo hazikan yan wasan a kasar baki daya.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng