Yawan cin Kilishi, Balango da Farfesu ke kashe Ýan Najeriya

Yawan cin Kilishi, Balango da Farfesu ke kashe Ýan Najeriya

Ministan kula da bangaren lafiya ta kasar nan Farfesa Isaac Adewole yace hawan jini shine abin da yafi hallaka yan Najeriya ta hanyar samar musu da ciwon zuciya.

Yawan cin Kilishi, Balango da Farfesu ke kashe Ýan Najeriya

Ministan ya bayyana haka ne yayin jawabin daya gabatar da taron da wata kungiya mai zaman kanta Tristate Heart Foundation (THF) ta shirya na samar da gidauniyar Naira miliyan 500 domin tallafa ma masu fama da ciwon zuciya a Najeriya.

Minista Adewole ya kara da cewa, sau dayawa cin abinci kowane iri shi ke janyo ciwon zuciya.

KU KARANTA:Hau! Uwa ta jefar da Jaririyarta a bola

Yayin da yake lissafo ire iren abinci dake kawo ciwon zuciya, Adewole yace “Yan Najeriya nada karancin halin cin abinci mai dauke da sinadaran gina jiki da karin jini, musamman kayan marmari da abincin ganye, wadanda sune ke kara yawan jini a jiki.

Yawan cin Kilishi, Balango da Farfesu ke kashe Ýan Najeriya
Farfesa Isaac

“abin takaicin ma yan Najeriya sun fi son cin abincin kan hanya masu saukin shiryawa, sa’annan da dama sun fi kaunar shan kayan zaki, kamar su lemun kwalba, taliya, alawa da sauran gangin siga. Bugu da kari, wasu kuma na yawan cin gishiri musamman a cikin irinsu balango, kilishi, farfesu da sauransu.” Inji Adewole.

Minista Adewole ya koka kan yadda jama’a ke rayuwa cikin munanan hali, inda yace alkalumma sun tabbatar da cewar mutuwa daga ciwon mutuwar jiki ya karu zuwa kashi 50 a watannin Ukun farko da kamuwa. Sa’annan Minista yace kashi 39 cikin wadanda suka wuce watannin ukun farko, suna mutuwa a shekaran farko, yayin da kashi 12 ke samun mummunan nakasa.

Ina tabbatar muku da cewa, mutum 5 a cikin mutane 10 na mutanen dake zaune a nan suna dauke da ciwon hawan jini, sa’annan sama da rabinsu basu san suna dauke da ciwon ba, inji Minista.

Kwararru sunce, yawan cin kayan abinci mai kitse, musamman na kifin ruwa na kara yiwuwar kamuwa da ciwon zuciya, ko na kumburin zuciya, da wasu nau’o’in ciwon daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel