Ramos ya kafa tarihi a wasan Elclasico

Ramos ya kafa tarihi a wasan Elclasico

- Kwallon da Sergio Ramos ya ci wa Real Madrid ya farke cin da Barcelona ta yi musu 1-1, a El Clasico ranar Asabar ita ce ta 75 da ya ci wa kungiya da kuma kasarsa

- Kwallon da ya ci a daidai karshen lokacin wasan ta sa ya zama dan wasan baya da ya fi cin kwallo, wanda yake buga wasa a wata babbar kungiya

Ramos ya kafa tarihi a wasan Elclasico

To amma duk da haka sai dai idan ya samu wani gagarumin cigaba, in ba haka ba, ba zai iya kawar da bajintar da ake da ita a tarihi ba.

Bajintar ita ce, ta tarihin da Kocin Everton Ronald Koeman, dan Barcelona a da, wanda ya ci wa kungiya da kasarsa kwallo 253.

KU KARANTA: Fellaini ya kwafsa a wasan Man Utd da Everton

Ciki har da kwallon da ta bakanta wa 'yan Ingila rai, wadda Koeman din ya ci daga bugun tazara a wasan da Holland ta ci Ingilan 2-0 na neman zuwa gasar kofin duniya ta 1994.

Ingila na neman ta ci wasan ta je gasar, kuma a dalilin rashin nasarar ba ta samu damar zuwa gasar ba.

Ronald Koeman, kanin tsohon kocin Feyenoord Erwin Koeman ne kuma dan tsohon dan wasan Holland Martin Koeman ne.

A hannu daya kuma, an haramta wa dan wasan Manchester City Sergio Aguero wasanni hudu bayan katin korar da alkalin wasa ya ba shi a wasan da Chelsea ta ci su 3-1 ranar Asabar a Etihad.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta tabbatar da hukuncin, sakamakon jan katin da aka ba shi.

Alkalin ya kori Aguero ne saboda yadda ya yi wa David Luiz keta lamarin da ya tayar da hatsaniya tsakanin 'yan wasan kungiyoyin biyu a kusan karshen wasan.

Tun a farkon wannan kakar an yi wa dan wasan na Argentina hukuncin haramcin wasanni uku saboda gula da ya yi wa Winston Reid na West Ham.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: