Shugaba Buhari zai yi balaguro kasar Senegal

Shugaba Buhari zai yi balaguro kasar Senegal

Nan bada dadewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Senegal don halartar taron samar da zaman lafiya a Afirka inda zai kwashe kwana daya a garin Dakar.

Shugaba Buhari zai yi balaguro kasar Senegal

Batun tafiyar shugaban na kumshe ne a cikin wata sanarwa data samu sa hannun mai magana da yawun shugaba Buhari Mista Femi Adesina, inda yace taron zai gudana daga ranar Litinin 5 ga watan Disamba zuwa Talata 6 ga watan Disamba.

Sanarwar tace “shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron tattauna batun samar da zaman lafiya da zai gudana a birnin Dakar kaso na Uku.

KU KARANTA: Ýan bindiga sun fatattaki Sarki daga fadarsa a jihar Ogun

“Taron da shugaban kasar Senegal Macky Sally tare da hadin gwiwar majalisar kasashen nahiyar Afirka suka shirya zata karkata ne wajen samar da dawwamammen zaman lafiya a nahiyar gaba daya, zai samu halartan shuwagabannin kasashen Afirka da wakilan kungiyoyin kasashe daban daban.

“Ana sa ran shugaba Buhari zai gabatar da kasida a yayin taron , a tsakanin shuwagabannin kasashen Afirka a ranar 6 ga watan Disamba. Shugaba Buhari nada tunanin cigaba mai daurewa ba zai samu ba face an samu dawwamammen zaman lafiya, zai gabatar da kasida dangane da kalubalen da ake fama dasu wajen samar da zaman lafiya musamman wajen yaki da ta’addanci, fashin teku, safarar yara da yan mata tare da amfani da miyagun kwayoyi.

“Sa’annan shugaba Buhari zai samu daman ganawa da shuwagabannin kasashe daban daban wajen hadin gwiwa don magance matsalolin tsaro a Najeriya.”

Daga karshe sanarwar ta karkare da “taken taron shine “yiwuwar gano bakin zaren kalubalen tsaron daya addabi yankin Afirka.”

Idan ba’a manta ba, a karshen watan Nuwamba ne shugaba Buhari ya kai ziyarar kwanaki 2 kasar Equatorial Guinea don halartan taron kasashen Afirka da na Larabawa karo na 4.

Zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng