Dan kasuwa ya bayyana abinda neman kudi ta sa shi
Frank yayin da yake bayyana labarinsa ga jaridar New Telegraph, “ni dan Aguleri ne a jihar Anambra. Inada wani yaya maikudi amma baya taimakawa kowa a dangi.”
Domin neman kudi, dan kasuwa igbo wanda ke kasuwar Ladipo a jihar Legas, Frank Obidinma yace yayi bacci wurare daban-daban domin yayi arziki da wuri.
Frank yayin da yake bayyana labarinsa ga jaridar New Telegraph yace : Ina cikin mawuyacin talauci,amma nace ba zanyi yan kan kai ba. Ni dan Aguleri ne a jihar Anambra. Inada wani yaya maikudi amma baya taimakawa kowa a dangi.
KU KARANTA: Abubuwan da suka faru a karshen mako (Karanta)
“Na kasance ina sayar da kayan mota ne a kasuwar Ladipo har lokacin da na fara asirin neman kudi. An hada ni da wata boka a jihar Kogi.
“An fada mini cewa bayan asirin, zanyi kudi na fitar hankali,sai na tai Igala wurin matan. Da naje Kogi ,sai aka fada mini in shiga cikin wani daji inda naga wasu suna neman kudi irina.mu kimanin shida ne
“Lokacin a muka fara asirin, an fada mana cewa duk wanda ya cika asirin zai yi kudi . ashe darasi zan koya mara dadi. An fada mana mu haka kabari. Da muka gama, ance zaá birnemu na tsawon kwanaki 3 cikin kabarin. Inda muka fito bayan kwanaki 3,zamuyi arziki.
“Na ji tsoro amma dan ina son kudi,kawai an shiga cikin makaran aka birne. Abin ba kyau,lokacin da aka fito da ni, wanda aka birne mu tare ya rigaya da mutuwa.
“Duk da hakan, sun ce mini ai kwana biyu kawai na ki . A lokacin ne na gano cewa ai da na karashe kwanaki 3 ,da na mutu.”
Ku biyo mu shafinmu na Tuiwita @naijcomhausa
Asali: Legit.ng