Wata yarinya mai shekara 10 a duniya ta zama uwa

Wata yarinya mai shekara 10 a duniya ta zama uwa

- Wata Yarinya mai shekara 10 ta haihu a Kasar Kenya

- Wannan yarinya ta zama ‘yar autan uwaye a bara

 Ko shin ta ina ta samu juna biyu?

Wata yarinya mai shekara 10 a duniya ta zama uwa

 

 

 

 

Wata karamar yarinya mai shekara 10 da haihuwa a duniya ta haifi wata itama. Wannan abin al’ajabi ya faru ne a Kasar Kenya a shekarar bara watau 2015.

Wannan yarinya mai shekara goma a duniya. Gladys Chelagat ta kafa tarihi, inda ta zama uwar da ta fi kowace karanci shekaru a duniya.

KU KARANTA: Wanda ba ta taba ganin namiji ba ta samu ciki

Likitoci dai sun ce Gladys ta sauka lafiya, inda ta haifi jariri mai nauyin kusan kilo uku. Sai dai da aka yi aiki, sannan aka samu cire jaririn da aka samu. An yi wannan aiki ne a wani Asibiti a Kasar Kenya.

Wani mutumi ne dai mai shekara 60 yayi wa wannan karamar yarinya ciki, wannan mutumi ya kasance mai kula da ita tun tana ‘yar karama. Wannana abu dai ya ba kowa mamaki kwarai da gaske. Wannan abu ya faru ne a Watan Yunin bara.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

 

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng