Tsohon mabaraci ya zama lauya

Tsohon mabaraci ya zama lauya

- Duk da kalubalen da ya fuskanta, Abdulsalam Idowu, ya je makaranta kuwa ya zamu digiri

- Abdulsalam Idowu ya zama lauya yanzu kuma yanada digri a harkokin siyasa

Tsohon mabaraci ya zama lauya

Wani tsohon mabaraci Abdulsalam Idowu, ya zama lauya yanzu inda aka yaye su a ranan laraba, 30 ga watan Nuwamba, a Abuja.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa Idowu duk da kalubalen da ya fuskanta a jam’iar Legas ya karashe karatun lauyarsa,inda yayi nasara a jarabawan na wannan shekara.

Idowu na daya daga cikin dalibai 4,225 da aka  yaye a makarantan horon lauyoyi a Abuja a ranan talata da laraba.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya sanya sabon ranar auren Zahra?

Lokacin da yake da shekarar 3, mahaifaiyar Idowu ta rasu, sannan kuma ya gurgunce. Kana mahaifinshi bai  damu da karatunsa ba, Idowu ya fara barar yana dan shekarar 8 a Erin Ile, jihar  Kwara.

Da yake da shekarar 37 a 2011, ya karshe karatu kimiyar siyasa daga jami’ar Legas amma wannan bai ishe sa ba. Sai ya garzaya ya fara karatun lauya.

“Ban gamsu lokain da aka bani kimiyar siyasa ba saboda lauya nike son zama. Sai na cigaba har na samu lauya.

"A shekarar 1987, ina dan shekarar 8 a ajin rauda.dukkan abokai na su cigaba zuwa aji daya amma ni na tsaya.

 "Da na tambayesu meyasa, suka ce ai ba’ayi mini rijista ba kawai sun barni inyi karatu da jarabawa ne .

"Da na koma gida nayi kira dukkan magabata nan a ce musu ina son ayi mini rijista amma sukace babu kudi kuma babu yadda zan iya karatu da gurgunci na.

 “Daga baya na fada musu su yi mini rijista kada su damu da kudin makaranta na. sai na fara bara domin samu in biya kudin makaranta.

 “Da na samu admisho a sheharar 1993, na kasa biyan kudin makaranta N520 amma ina jin ana cewa ana samun kudi a jihar Legas. Wata ranan sai na shiga jirgin kasa na je legas na fara bara. Sai na fara zama a karkashin gada tare da wasu mutane inda nayi bara a wurare da dama.

A biyomu shafinmu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel