Dan kwallon Afrika daya ne a jerin gwanayen duniya

Dan kwallon Afrika daya ne a jerin gwanayen duniya

- An bayyana sunayen gwanayen 'yan kwallon kafa na duniya 55, da za a zabi 11 daga ciki, kuma dan Afrika daya ne kawai Serge Aurier dan Ivory Coast da PSG, Ingila ma, Jamie Vardy na Leicester ne kawai

- Jerin 'yan wasan da ake wa lakabi da FIFpro hadaka ce ta 'yan wasan kwallon kafa na duniya, da kwararrun 'yan wasa dubu 25 daga kasashe 75 suke kada kuri'ar zabo su

Dan kwallon Afrika daya ne a jerin gwanayen duniya

Paris St Germain da Ivory Coast Serge Aurier, shi kadai ne daga Afrika ya kasance cikin 'yan wasan.

KU KARANTA: Kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya ta kai wasan karshe

Jamie Vardy mai shekara 29 na Leicester wanda shi kadai ne dan wasan Ingila da ke cikin jerin, ya samu shiga ne bayan da ya ci kwallaye 24, ya taimaka wa kungiyarsa ta dauki Premier a kakar da ta wuce.

A karon farko a shekara 12 ta tarihin gasar kyaftin din Ingila Wayne Rooney bai samu shiga ba, amma dan wasan Real Madrid na Wales Gareth Bale a karo na biyu a jere ya samu shiga.

Cristiano Ronaldo da golan Juventus Buffon kamar kowace shekara sunansu na ciki.

Jumulla 'yan wasan Premier 16 ne suka samu shiga jerin, wadanda suka kunshi tsohon dan Leicester N'Golo Kante wanda ke Chelsea yanzu.

Sai Kevin De Bruyne na Manchester City da Dmitri Payet na West Ham da Hector Bellerin na Arsenal.

Barcelona tana da 'yan wasa 12, inda ta zarta abokiyar hamayyarta Real Madrid mai guda goma.

A ranar tara ga watan Janairu ne a birnin Zurich, za a bayyana sunayen guda 11 da aka reraye a ciki.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel